
Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi lambar yabo daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, bisa nasarorin da ya samu a fannin tsaro da inganta dimokuradiyya a yankin.
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata cewa, Umaro Sissoco Embalo, shugaban kungiyar ECOWAS ne ya sanar da hakan a ganawar da suka yi da Buhari a gefen taron majalisar dinkin duniya karo na 5 kan kasashe mafi karancin ci gaba a Qatar.

Ana sa ran Buhari zai dawo kasar a ranar Laraba 8 ga Maris, 2023.
Shehu ya ruwaito Embalo na cewa shugaban Najeriya ya yi fiye da kowa wajen goyon bayan gwamnatocin dimokaradiyya a Afirka ta Yamma kamar yadda ya yi nasa na musamman a yakin da ake yi da ‘yan tawaye, bullar gwamnatocin da ba na demokradiyya ba.

Shugaban ECOWAS ya ce Buhari zai sanya sunansa a cikin “Roll of Honour” a sabon ginin hedikwatar al’umma bayan an kammala shi a Abuja.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai