INEC Ta Sanar Da Mal Shekarau Wanda Ya Lashe Kujerar Sanatan Kano Ta Tsakiya


Alfijr ta rawaito Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar NNPP.

Baturen zaben Farfesa Tijjani Hassan Darma ne ya bayyana Sanata Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a 456,787 akan babban abokin karawarsa na Jamiyyar APC Abdulkarim Abdussalam Zaura wanda ya sami kuri’a 168, 677.

A baya dai Sanata Malam Shekarau shi ne wanda Jam’iyyar NNPP ta fara tsayarwa a matsayin dan takararta a kujerar sanatan Kano ta Tsakiya kafin daga bisani ta maye gurbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga sakamakon barin Jamiyyar ta NNPP da Shekarau din ya yi.

Lamarin da ya jefa mutane da yawa cikin rudani, inda magoya bayan jam’iyyar ta NNPCL suke cewa ba za ta sabu ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux


4 Replies to “INEC Ta Sanar Da Mal Shekarau Wanda Ya Lashe Kujerar Sanatan Kano Ta Tsakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *