Yanzu-Yanzu Ƴan Daba Sun Mamaye Rumfunan Zabe Sun Kona Akwatin Zabe

Alfijr ta rawaito ƴan daba daba sun yi wa wasu rumfunan zabe a yankin Oshodi da Itire a Legas kawanya, tare da banka wasu katin zabe da kuma cinna wuta.

Ƴan barandan wadanda dukkansu sanye da bakaken kaya da rufe fuska, sun isa yankin ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Asabar.

Wasu masu kada kuri’a, wadanda ba su iya guduwa ba lokacin da ‘yan barandan suka iso sun ji rauni.

Majiyoyi sun ce ‘yan barandan, daga baya sun zagaya yankin, mintuna kadan bayan wasu jami’an tsaro da ke aikin zabe sun bar aikinsu.

A cewar Tajudeen Haruna, bayan mintuna kadan ne ‘yan barandan suka bude wuta tare da tsorata masu kada kuri’a.

“Daga baya ne ‘yan barandan suka cinna wa akwatin zabe da wasu kayayyaki wuta,” in ji shi.

Hakazalika, wasu ‘yan baranda sun kai farmaki yankin Itire, da misalin karfe 12 na dare, inda suka tsorata masu kada kuri’a daga sassa daban-daban na yankin.

James Nwoke, ya yi zargin cewa da gangan ne aka yi yunkurin bata wa wadanda ba ‘yan asalin jihar hakkinsu ba.

A halin da ake ciki, akwai dimbin sojoji da ‘yan sanda a cikin birnin Legas ranar Asabar don dakile tabarbarewar doka da oda.

A lokaci guda kuma, samari sun mayar da hanyar motar Agege da Apapa-Oshodi, Okota da wasu sassa na fadar Ago hanyar zuwa filin wasan kwallon kafa.

Ana kuma samun tashin hankali a mafi yawan yankunan Ago, Isolo da Ire-Akri biyo bayan gazawar wasu masu kada kuri’a wajen gano wuraren zabensu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *