Alfijr ta rawaito hukumar hisba reshen jihar Kebbi ta yiwa wani matshi aski mai taken talkobo a babban birnin jihar Kebbi, Birnin Kebbi.
Matashin yaron wanda kansa ke dauke da askin suwaga ya shiga hannun hisbar ne a yau laraba 15 ga watan fabrairu 2023 inda hukumar ta bayyana hakan a shafinta na sada zumunta na Facebook.
Matashin mai suna Mubarak dan asalin jihar Kebbi ne mazaunin unguwar badariya, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Mai girma ubandoman gwandu Alh. Sa’ad ne ya bayar da umarnin yi wa Mubarak din aski.
Hukumar hisba ta dauki aniyar aske kan duk wani mai askin banza a fadin jihar kebbi musamman a birnin
Hisba ta samu umarni daga Uban doma da yiwa duk wanda aka samu da askin banza aski a birnin kebbi.
ALLMEDIA24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇