Alfijr ta rawaito Gwamnatin Najeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar gabanta na haramta daina karbar 200 da 500 da kuma 1,000 a ranar 10 ga watan Fabarairu.
Ranar Laraba ne dai kotun ta bayar da umarnin a dakata da amfani da wa’adin har zuwa ranar 15 ga watan na Fabarairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar suna kalubalantar wa’adin.
Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Najeriyar, Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a yayin wata hira da tashar talabijin ta Arise TV, a jiya Alhamis.
Ya kara da cewar, yana fatan idan aka koma sauraren shari’ar Kotun Kolin za ta soke wannan umarni, wato ta bar Babban bakin ya aiwatar da tsarinsa na sanya wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin da bankin ya sauya.
Malami ya kara da cewa kasancewar Babban Bankin wanda kusa ne a shari’ar, wanda kuma ba a sanya shi ba a cikin karar da gwamnonin suka shigar, hakan ya sa a Kotun Kolin ba ta da hurumin yanke hukunci a kan batun tun ma da farko a cewarsa.
Amma kuma ya ce gwamnati ta yanke shawarar bin umarnin Kotun Kolin ne domin mutunta doka da oda.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
An kyauta.