Alfijr ta rawaito wata kotun hukunta laifukan lalata da maza da mata a Jihar Lagas ta yankewa wani malamin Islamiyya, Adam Farouk, hukuncin daurin rai da rai, bisa samunsa da laifin lalata da dalibansa takwas ‘yan kasa da shekaru shida.
Mai shari’a Soladoye Abiola, ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da babu shakka a cikin tuhume-tuhume takwas da suka hada da cin zarafi ta hanyar yin lalata da malamin ya yi, da daliban.
Mai shari’a ya bayyana malamin a matsayin wanda bai da tarbiyya kuma abin kunya ga Addinin Musulunci, inda ya bayyana cewa an tabbatar da hujjojin da suka nuna yadda ya yi amfani da hannunsa wajen lalata daliban.
Wata shaida ta ce wanda ake tuhumar ya umarci yaran da su juya baya yayin da yake lalata su da yatsansa.
“Ana sa ran ya koya wa dalibansa dabi’u, da’a da kuma tarbiyya, amma sai aka samu akasin haka, abin da ya aikata abun ki ne.
“An yanke wa wanda ake tuhumar da dukkan tuhume-tuhumen, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kan kowanne daga cikin laifuka takwas amma hukuncin zai gudana a lokaci guda.”
Mai shari’a ya kuma bayar da umarnin a rubuta sunan mai laifin a cikin rajistar masu aikata laifuka ta jihar Lagos.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇