Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da cire N499,650,000 daga asusun hadin gwiwa na jihar domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron jihar, yayin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a jihar.

Wata majiya ta bayyana cewa ana sa ran Buhari zai jagoranci jiga-jigan jam’iyyar APC da magoya bayan jam’iyyar a Katsina tsakanin ranakun Juma’a da Asabar 26 da 27 ga watan Janairun 2023.
Gabanin taron, wata wasika da ake zargin an aikewa da Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar Katsina da kuma Harkokin masarautu da sakatariyar dindindin mai kula da gidan gwamnati ya sanya wa hannu, ta tabbatar da amincewar Gwamna Masari na cire wasu makudan kudade daga asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi.
“An umurce ni da in mika wasikar ku mai lamba S/MLGCA/GEN/259/C/IV ta 17” Janairu 2023 da kuma isar da amincewar mai girma Gwamna, na a saki N14,695,588.00 ga kowane mutum 34.
Kananan Hukumomin sun kai N499,650,000.00 (Miliyan dari hudu da casa’in da tara, Naira dubu dari shida da hamsin kacal) daga cikin ma’auni na kananan hukumomi 34 dake cikin asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi domin baiwa kananan hukumomin damar samar da isasshiyar hadakar ‘yan kasa, su karbi bakuncin shugaban kasa a ziyarar aiki jihar Katsina daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairu, 2023,”
Wasikar mai dauke da sa hannun babban sakataren gidan gwamnatin Katsina mai kwanan wata 18 ga Janairu, 2023.
Takardar ta kara da cewa, an aika da wannan wasika zuwa ga Akanta Janar, Ma’aikatar Kudi da Audita Janar na Kananan Hukumomi don masaniyarsu.
Idan za’a tuna a baya kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta bayyana cewa shugaba Buhari zai jagoranci magoya bayan jam’iyyar a yakin neman zaben Tinubu a fadin jihohi 10 na tarayyar kasar nan.
Jihohin sun hada da Adamawa, Yobe, Sokoto, Kwara, Ogun, Cross Rivers, Nasarawa, Katsina da Imo, da kuma babban zaben da aka shirya gudanarwa a jihar Legas.
Naija News
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Allah sarki talakawan Nigeria muna cikin damuwarda yakamata shugabanninmu sufidda kudi autaimakemu Amma bazasuyiba saigashi ashirme tunda harkar biyan bukatunsuce zasu debe kudin talakawa subiya bukatarsu dashi Allah yayimana magani.