Alfijr ta rawaito Kimanin mutane 25 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar diphtheria wadda wasu suke kira mashako ko sarkewar numfashi a Kano zuwa Juma’ar da ta gabata.
Solacebase ta tattaro cewa cutar nan mai kashe kananan yara da aka fara gano ta a Kano a karshen shekarar da ta gabata ana kula da ita kamar yadda ta bulla a Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, AKTH, a Kano.
An fara samun cutar ne daga karamar hukumar Ungogo da ke Kano.
A cewar ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, an samu rahoton mutane 58 da ake zargin sun kamu da cutar, 6 kuma sun kamu da cutar, yayin da majinyata 25 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar diphtheria a ranar 13 ga Janairu, 2023.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewar da yawan barkewar cutar, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa, NCDC a makon da ya gabata, nan da nan ta tura jami’ai zuwa Kano don kafa tsarin bayar da umarni don gudanar da bincike game da cutar diphtheria, ba da tallafin fasaha da kuma sake farfado da cibiyar aiki don jinya.
“Kamar yadda muke magana yanzu, Médecins Sans Frontières (MSF) wacce aka fi sani da Doctors without borders, ta kafa cibiyar kula a Asibitin Murtala Muhammed kuma tana ba da magunguna masu mahimmanci.
Wani mai ba da shawara kan harkokin kiwon lafiya da ya nemi a sakaya sunansa ya danganta bullar cutar da gazawar allurar rigakafin da aka saba yi a Kano.
Masanin ya ce, akwai karancin aikin rigakafi a Kano, wanda shi ne babbar hanyar rigakafin barkewar cutar, tare da karancin sanin jama’a.
“Kun ga idan an gudanar da kula da wadannan cututtuka ta hanyar fadakar da mazauna yankin, da hakan zai rage yaduwar cutar a tsakanin kananan yara,” in ji masanin likitancin.
“A yanzu haka an samu bullar cutar zazzabin Lassa, daga karamar hukumar Dala a makon jiya.
Ya kara da cewa Jihar ba ta yin abin da ya dace wajen wayar da kan jama’a domin a dakile yaduwar cutar ba.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase a ranar Alhamis.
Tsanyawa, ya ce an kaddamar da kwamitin shirye-shiryen gaggawa na jihar har ma ya bayar da agajin gaggawa, ya kuma kira taro a safiyar yau don tantance alkaluman wadanda suka mutu, da sake duba bayanai da matakan magance lamarin.
Ƴa kara da cewar, a halin yanzu, an sake farfado da kungiyar masu ba da agajin gaggawa ta jihar kuma an tanadi shirin aiwatar da aikin duba yaduwar cutar diphtheria.
“Yanzu haka mun gabatar da kasafin kudin ga gwamnati kuma an amince da shi,” in ji Kwamishinan
Ya ce karancin allurar rigakafin da ake dangantawa da yaduwar cutar ya samo asali ne sakamakon wahalar isa ga yankunan jihar.
Ya yi nuni da cewa, duk da haka, jihar na kara karfafa allurar rigakafin da ta saba yi.
Tsanyawa ya ce baya ga asibitin kwararru na Murtala Muhammad da aka kebe a matsayin cibiyar keɓewa, za a samar da wasu cibiyoyin keɓewa don duba yaduwar cutar.
“Duk da cewa mun yi amfani da Yargaya don keɓewar COVID-19, mun keɓe wurin don keɓe masu kamuwa da cutar diphtheria kuma.”
”Kada mutane su firgita amma idan suka ga wani zazzabi da ba a saba gani ba, to a gaggauta zuwa asibiti.”
”Mun riga mun fara wayar da kan jama’a kan cutar.”
Solacebase
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇