Kotu Tayi Sammacin Gwamnan Babban Bankin Najeriya


Alfijr ta rawaito Babbar Kotun birnin tarayya Abuja ta sammaci Gwamnan Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele, da ya bayyana gabanta ranar Laraba dangane da shari’ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’

Hakan na zuwa ne biyo bayan wata kara da karar da lauya Joe Agi, ya shigar a kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi, da ya shigar gaban kotun ranar 20 ga watan Oktoban 2022, gaban  Mai Shari’a Inyang Ekwo

Alkalin ya bai wa Emefiele Umarnin ya bayyana a gaban kotun ran 18 ga Janairu don sauraron shari’ar zargin da ake masa.

Kunshin karar na neman kotu ta bai wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda odar cafke Emefiele da lauyoyinsa tare da gabatar da su ga kotu.

Karar ta taso ne kan hukuncin Dala miliyan 70 da aka yanke wa Linas kan ayyukan lauyoyi game da kudin Paris Club, wanda aka ce Emefiele ya saki Dala miliyan 17 sannan Dala miliyan 53 sun makale.

A ranar 23 ga Janairu, 2020 kotu tayi Umarnin cewa dole Emefiele ya bayyana gabanta, domin yi masa shari’a kan rantsuwar da ya shafi hanyoyin da yake da su ko kuma ya samu, tun daga ranar da aka ba da cikakken umarni, na biyan bashin Dala miliyan 53 a halin yanzu, kuma za a biya a karkashin wannan umarnin kuma ya nuna dalilin da ya sa ba za a tura shi kurkuku ba na rashin biyan kudin.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

One Reply to “Kotu Tayi Sammacin Gwamnan Babban Bankin Najeriya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *