Ƴan Bindiga Sun Harbe Sufeton Ƴan Sanda Sun Kuma Ƙwace Bindiga Daya

Alfijr ta rawaito an kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar tsaro ta Gabas, ESN ne da laifin kashe wani sufeto ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Ndiegoro da ke Aba, jihar Abia.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren ranar Talata a hanyar Ohanku, mahadar Iheorji a Aba.

A lokacin da lamarin ya faru, ‘yan sanda sun kashe biyu daga cikin maharan a fafatawa da suka yi.

NAN ta bayyana cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ogbonna ya ce wasu ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Ndiegoro suna sintiri a kewayen Iheorji lokacin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ESN/IPOB ne suka kai musu hari.

“A yayin da aka yi musayar wuta da bindiga, daya daga cikin ‘yan sandan ya biya farashi mai Tsoka don fansar kansa, yayin da aka kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar.

“Yayin da suka harbe dan sandan, sun kuma karbo bindigar AK-47 na ‘yan sanda,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *