Yadda Ta Kasance A Shari’ar Balaraba Ganduje Da Mijinta Inuwa A Yau

Alfijr ta rawaito Surukin Ganduje, Inuwa Uba, ya kalubalanci hurumin kotun da matarsa, Balaraba Ganduje, ta maka shi, tana so a datse igiyar aurensu.

Ya bayyana hakan ne a yayin zaman Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hokey da ke Kano, ranar Alhamis.

Tun farko dai Balaraba Ganduje ce ta maka mijin nata a gaban kotun tana neman a raba auren nasu, duk da cewa sun shafe shekara 16, tare da ’ya’ya hudu.

Balaraba, ta bakin lauyanta Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa, ta shaida wa kotun cewa ta yi wannan nema ne gaban kotun a karkarshin sashen Shari’ar Musulunci wato ‘Khul’i’ wanda ya ba mata damar fansar kansu daga mazajensu.

Barista Aliyu ya bayyana cewa sun shaida wa kotun cewa, duk da cewar ba su bayyana wa kotun dalilansu na son rabuwar auren ba, amma sun ce a shirye suke su biya wanda suke kara sadakinsa na Naira dubu 50.

Sai dai a zaman da ya gudana ranar Alhamis, lauyoyin wanda ake kara karkarshin jagorancin Barista Umar I. Umar, sun kalubalanci cewa kotun ma ba ta da hurumin sauraren shari’ar.

Hakan ya sa lauyoyin masu kara suka nemi kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci don su mayar wa wadanda ake kara martani.

Alkalin kotun Mai shari’a Khadi Abdullahi Halliru ya sanya ranar 12 ga Janairu, 2023 don sauraren martanin masu kara.

Sai dai lauyan wadanda ake karar ya ce har gobe wanda yake karewa na neman bikon matar tasa, domin su koma su ci gaba da zaman aure, amma ita ta ki amincewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *