Ɗan Bindiga Ya Harbe Ɗan Sanda Ya Kuma Ɗauke Bindigarsa

Alfijr ta rawaito an harbe wani ɗan sanda har lahira sun kuma ɗauke bindigarsa a harabar wani banki da ke kan titin DSP Alamieyeseigha a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Majiyar ta bayyana cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare.

Rahotanni sun kara da cewa, wanda ake zargi da kisan, marigayin, ya gabatar da shi ga jami’an banki a matsayin dan uwansa wanda ya bayyana sunansa da David.

A cewar majiyoyin, wanda ake zargi da kisan ya kasance tare da marigayin a bankin inda ya ke gadi har tsawon mako ɗaya, inda a ka ce “Al’amarin ya faru ne a lokacin da su biyun ke cin abinci.

Yayin da dan sandan ya ajiye bindigarsa a kan benci ya na wanke cokalin da za su ci abincin, sai shi David ɗin ya dauki bindigar ya harbe shi a daf da daf,” inji wata majiya.

Nan take aka garzaya da shi asibitin tarayya inda aka tabbatar da rasuwarsa washegari.

A cewar majiyar, tuni ‘yan sanda su ka fara gudanar da bincike kan lamarin tare da kokarin kwato bindigar da aka sace.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Butswat ya ruwaito cewa: “A ranar 29 ga Disamba, 2022, wani dan sanda, Cpl Bob, da ke bakin aiki a wani banki a Yenagoa ya mutu bayan da wani da su ke tare ya harbe shi a harsbsr bankin.

“An san ainihin wanda ake zargin kuma ana bincike,”

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *