Alfijr ta rawaito Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta sami nasarar kama masu laifi 3,245 daga watan Janairu zuwa Disambar 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da
Kakakin yaɗa labarai na hukumar ne, Nabilusi Abubakar, ya fitar da wata sabuwar a ranar Juma’a a Kano.
Ya Kara da cewar an sami ragin masu aikata laifin a shekarar 2022, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata da KAROTA ta samu masu laifi 7,835.
Sanarwar ta ce, “shekarar da ake shirin bankwana da ita, hukumar ta yi nasarar yi wa adadin masu ɗan sahu 52,242 rajistar izinin tuki na Kano.
“Wannan rajistar tana da matukar muhimmanci a gare mu, don haka duk wanda aka yi wa babur dinsa rajistar ba zai yi amfani da ita wajen aikata laifi ba, ya sani sarai za a kama shi.
Hakazalika jami’anmu sun kama masu aikata laifuka daban-daban daga cikin masu wannan sana’ar.
Kuma sun sami nasarar kamo barayin waya da dama ta hanyar wannan Rijistar a fadin jihar.
Abubakar ya ce hukumar ta samu nasarar daukar sabbin ma’aikata sama da 500, wanda hakan ya kara mana kwarin gwiwa a jihar, tare da samar da sabbin ofisoshin shiyya a Tudun Wada da Doguwa.
A cikin shekarar majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, ta 2022. In Ji shi.
Ya ƙara da cewa, hukumar ta samu takardar sammacin kotu na samun nasarar rusa haramtattun gine-ginen da suka toshe hanyoyi a cikin kwaryar birni da kuma wasu manyan kasuwanni wadanda suka hana zirga-zirgar ababen hawa.
Nabulisi ya rufe da nuna godiya ga jama’a tare da ba su tabbacin za su zage damtse wajen yin aiki a shekara mai zuwa don kare su yayin amfani da hanyoyin a jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇