Alfijr ta rawaito Jami’an ƴan sanda sun gurfanar da Franklin Poroye da Adedayo Ayodele a gaban Kotun Majistare da ke zamanta a yankin Ejigbo na Jihar Legas kan mallakar shaidar zama likita bogi, da zarginsu da hadin baki, cuta, tare da zamba.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Benedict Aigbokhan, ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar daya ga watan Janairun 2022, a asibitin Jumoke da ke Orisunbare Shasha a Lagos.
A cewarsa, mutanen biyu sun yi amfani da shaidar likita ta bogi wajen neman aiki a asibitin, wanda ya ce hakan ya saba wa doka, hakan na iya cutar da marasa lafiya a asibitin.
Laifin ya saba wa tanade-tanaden sassa na 166 da na 365 da na 380 da kuma na 411 na kundin laifuka na 2015 na Jihar Legas. In Ji shi
Mai Shari’a K. A. Ariyo, ta bayar da belin kowanensu a kan kudi Naira 500,000 tare da gabatar da wadanda za su tsaya musu.
Alkalin ta ce dole ne wadanda za su tsaya musu, su kasance masu aikin yi sannan daya cikinsu ya kasance dan uwa shakiki na kowane daga cikinsu.
Kotun ta ce dole ne wadanda za su tsaya musu su gabatar da shaidar biyan haraji ta Gwamnatin Jihar Lagos.
Daga nan sai ta dage sauraren karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2023 mai zuwa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇