Alfijr ta rawaito an kama wani likita da ya tono sassan jikin mutane daga kaburbura a cikin makabartar Katolika da ke Ajaba Mmaku, a karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.
A cewar rahotanni a ranar Asabar, 10 ga Disamba, 2022, an kama likitan dan kasar tare da wasu mutane uku masu taimaka masa laifin
An ce wani mai kula da sashen biredi da ke harabar cocin ne ya kama wadanda ake zargin suna yankar sassan jikin mutane a makabartar.
Wadanda ake zargin bayan sun lura cewa mai burodin ya gansu, sai suka yi gaggawar yi masa alkawari mai tsoka matukar bai tona su ba.
Komawarsa ke da wuya ya sanar da firist wani shugaba ne mai kula da cocin.
Majiyoyin al’umma sun ce wadanda ake zargin da ganin limamin cocin da wasu mutane, suna ta kai kawo.
“ Ganin haka aka sanar da ‘yan banga na yankin Mmaku, ba suyi ƙasa a guiwa ba suka garzayo da gudu suka kama guda uku daga cikin su, sannan daya ya tsere.
“Wadanda aka kama sun hada da Aloysius Okeke (aka Aloy Ojoma), Israel Okoli, da Amaechi Udeji, dukkansu ‘yan kauyen Enugu Afam dake yankin Agunese Mmaku ne.
A halin da ake ciki kuma, majiyar ta ce an dade ana gudanar da farautar wanda ake zargi da guduwa, inda ta ce an dade ana gudanar da harkokin kasuwanci na samun sassan jikin dan adam don gudanar da ayyukan ibada a cikin al’umma da kuma makwabta.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu DSP Daniel Ndukwe ya ci tura domin bai amsa kiran da ya yi masa ba har ya zuwa lokacin mika wannan rahoton.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda ko a’a.
[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Allah yatseratar damu fadawa halaka yakuma karemana imaninmu yasamu muyi kyakykyawan karshe ameen.