
Alfijr ta rawaito fitattun ƴan Kasuwa ‘Dan Kasuwa Kuma masu Tallafawa Al’umma, Alhaji Aminu Dantata, da Abdulsamad Rabiu, wanda ya kafa kungiyar BUA, a ranar Asabar, sun tara sama da Naira biliyan daya ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jigawa.
An bayar da tallafin ne a garin Dutse a wajen wani asusun tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a shekarar 2022.
Dantata da Rabiu kowanne ya bayar da Naira miliyan 200, gwamnatin jihar Jigawa Naira miliyan 250, Gwamna Muhammad Badaru, ya bayar da Naira miliyan 25 a madadin kansa da iyalansa da kuma kamfaninsa na Talamis Group.
Sai dai Dantata wanda ya samu wakilcin Alhaji Salisu Sambajo ya nuna damuwarsa kan halin da wadanda ambaliyar ta shafa suka tsinci kansu a ciki bayan afkuwar lamarin.
Mai taimakon ya yi addu’a ga wadanda suka mutu a lokacin bala’in tare da tausaya wa wadanda suka yi hasarar dukiyoyinsu da amfanin gonakinsu a ambaliyar.
Hakazalika, Badaru ya kuma nuna jin dadinsa ga dimbin masu hannu da shuni bisa wannan karimcin da suka nuna, ya kuma bukaci kwamitin tara kudaden da su kasance masu adalci wajen rabon kayan agaji da kudade.
Shugaban kwamatin, Alhaji Bashir Dalhatu, (Wazirin Dutse) kuma tsohon ministan wutar lantarki, ya godewa daidaikun jama’a da gungun kamfanoni bisa tallafawa wadanda abin ya shafa.
Sauran masu bayar da tallafi sun hada da ‘yan majalisar jiha da na kasa da kuma shugabannin kansiloli.
Bankin Zenith, Bankin Jaiz, FCMB, Sterling Bank, GTBANK da Unity Bank na daga cikin cibiyoyin hada-hadar kudi da suka bayar da gudunmawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ