Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta ce ba ta soke ko haramta sana’ar downloading a faɗin jiha ba, duk da rahotannin da ke yawo cewa an dakatar da sana’ar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a ranar Alhamis 16-07-2026.
Sanarwar ta ce babu wata hukuma da ta tuntuɓi hukumar tace Fina-finai da dab’i kafin ɗaukar irin wannan mataki, duk da cewa masu sana’ar downloading na daga cikin waɗanda hukumar ke da alhakin sa ido kan ayyukansu bisa tanadin dokar da ta kafa ta.
Haka kuma Hukumar ta ce tuni ta fara bincike kan wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin wasu masu sana’ar da yaɗa bidiyoyin tsiraici ko. Sai dai ta ce binciken farko ya nuna cewa ana zargin muryar da ke cikin saƙon ba daga Jihar Kano take ba, yayin da bincike ke ci gaba.Geographic Reference
A cewar sanarwar, hukumar ta tura jami’anta a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin gano masu yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya, tare da ɗaukar matakin doka a kansu idan aka same su da aikata laifi.
Hukumar ta kuma ce ta yi la’akari da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin masu sana’ar downloading da masana’antar Kannywood, tare da muhimmancin samar wa matasa hanyoyin samun abin dogaro da kai. Saboda haka, ta jaddada cewa ba ta haramta sana’ar ba, sai dai za ta ci gaba da hukunta duk wanda aka kama yana amfani da ita wajen yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.
A ƙarshe, hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta buƙaci jama’a su ci gaba da ba ta haɗin kai tare da kai mata sahihan bayanai domin tabbatar da bin doka da oda a jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
