Ibtila’i! Sama da gidaje 200 ne suka lalace sakamakon Ruwan sama kamar da bakin kwarya da mai Iska a birnin Dutse

FB IMG 1783425328671

Wani mamakon ruwan sama da ya ɗauki sama da awa gada ya haddasa ambaliya a sassa daban-daban na birnin, ciki har da Dan Masara, hanyar zuwa Fadar Gwamnatin Jihar da kuma Takur.

Wani mazaunin Dutse, Abdullahi Kamilu, ya ce ambaliyar ta lalata gidaje, makarantu, wuraren kasuwanci, masallatai da kuma turakun wutar lantarki, lamarin da ya jefa al’umma cikin matsananciyar wahala.

A martaninta, Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba kayan aikin tsaftace magudanan ruwa, da suka haɗa da baro, manjagara da shebur, domin taimaka wa mazauna yankunan da abin ya shafa wajen rage illar ambaliyar da kuma buɗe hanyoyin ruwa.

Tun a shekarar 2025 hukumomin gwamnati suka yi hasashen cewa birnin Dutse na daga cikin wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliya, inda suka bayyana cewa yankuna 148 a ƙananan hukumomi 17 na jihar na cikin haɗarin ambaliyar ruwa.

Alfarma Radiyo

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *