Babban Bankin Najeriya, CBN, ya soke lasisin aiki na ƙananan bankunan Microfinance Bank guda 46 daga ranar 1 ga watan Yuli, 2026.
Bankin ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda bankunan sun gaza cika wasu muhimman ƙa’idojin gudanar da harkokin banki, da suka haɗa da rashin isassun kadarori, dakatar da aiki ba tare da izini ba, daina gudanar da harkokin banki, da kuma kasa cika mafi ƙarancin jarin da ake buƙata.
CBN ta ce matakin na da nufin kare kuɗaɗen masu ajiya da kuma tabbatar da inganci da kwanciyar hankali a tsarin harkokin kuɗi na ƙasar.
Daga cikin bankunan da abin ya shafa akwai Zain, Bompai, Ajwa, NOW NOW Digital, Minjibir, Shanono, Sumaila, Rimin Gado, Sycamore, TOFA, Kanopoly, Bellbank da Esteem, waɗanda dukkansu ke da hedikwata a Jihar Kano.



Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t