Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa tun kafin gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumi kan wani mai sana’ar canjin kuɗi a Legas, Mukhtar Adamu Muhammad, da wasu kamfanoni uku masu alaƙa da shi, tana gudanar da bincike a kansu kan zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Majiyoyi daga cikin hukumar EFCC sun bayyana cewa binciken da ake yi kan Mukhtar Adamu Muhammad da kamfanonin canjin kuɗin ya kai matakin ƙarshe, har ma ana shirin gurfanar da su a kotu lokacin da Amurka ta sanar da sanya musu takunkumi.
Matakin na Amurka ya biyo bayan zargin cewa Mukhtar Adamu Muhammad da wasu kamfanoni uku na Najeriya sun taimaka wajen gudanar da harkokin kuɗaɗe ga ƙungiyar ta’addanci ta ISIS.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, an ce takunkumin ya shafi wasu mutane da kamfanoni a ƙasashe daban-daban da suka haɗa da Faransa, Siriya, Turkiyya da Najeriya.
Sanarwar ta bayyana Mukhtar Adamu Muhammad, wanda aka fi sani da Mukhtar Muhammad, a matsayin mai gudanar da sana’ar Bureau De Change a Jihar Legas, tare da zargin cewa shi da kamfanonin da ke da alaƙa da shi sun taimaka wajen safarar kuɗaɗe ga reshen ISIS da ke Yammacin Afirka.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t