Ofishin Jakadancin Masarautar Saudiyya da ke Abuja, ta hannun Cibiyar Agaji da Tallafin Jinƙai ta Sarki Salman (KSrelief), tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun ƙaddamar da Shirin Tallafin rabon kayan Abinci na shekarar 2026 domin tallafa wa al’ummomin da suka fuskanci matsalolin ƙaura, rashin tsaro da sauran ƙalubalen jinƙai a faɗin Nijeriya.
A ƙarƙashin wannan shiri, za a raba kwandunan abinci guda 24,302, inda kowanne yake da nauyin kusan kilogiram 60, kuma ya ƙunshi muhimman kayan abinci kamar shinkafa, man girki, farin wake, gishiri da sauran kayan masarufi na yau da kullum.
Shirin, wanda darajar sa ta haura dalar Amurka miliyan 1.5, ana sa ran zai amfani mutum 145,812 a al’ummomi daban-daban na ƙasar nan, tare da samar da agajin da ake matuƙar buƙata ga gidajen da ke fama da ƙarancin abinci.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin a Damaturu, Darakta Janar na NEMA ya sake jaddada aniyar hukumar na tabbatar da an raba kayan abincin cikin gaskiya da inganci ga waɗanda aka tantance za su amfana, daidai da nauyin da ya rataya a wuyan ta na daidaita ayyukan agajin bala’o’i da tallafin jinƙai a Nijeriya.
Za a raba kwandunan abincin a jihohi biyar da aka zaɓa domin aiwatar da shirin, wato Yobe, Binuwai, Anambra, Kebbi da Taraba.
Wannan shirin tallafin abinci ya sake nuna ci gaba da jajircewar Masarautar Saudiyya ke yi wajen bayar da agajin jinƙai da tallafa wa al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a Nijeriya da yankin Tafkin Chadi.
Ta hannun KSrelief, Saudiyya tana ci gaba da samar da muhimman ayyukan agaji domin inganta wadatar abinci da rage wahalhalun da al’ummomin da rikice-rikice suka shafa ke fuskanta.
Haɗin gwiwar da ke tsakanin NEMA da KSrelief ya nuna muhimmancin haɗin kan ƙasa da ƙasa wajen tunkarar ƙalubalen jinƙai da kuma tallafa wa al’ummomin da ke cikin buƙata.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t