Jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomi da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Adamawa (ADSIEC) ta gudanar, inda ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 na jihar.
Baya ga haka, jam’iyyar ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 226 da ke fadin gundumomin jihar.
Rahotonni sunce sakamakon karshe ne a ranar 15 ga Yuni, bayan kammala zaben karamar hukumar Numan, wanda aka dage daga ranar Asabar lokacin da aka gudanar da zabe a sauran kananan hukumomi 20.
Da yake bayyana sakamakon zaben Numan, jami’in zaben yankin, Sani Ahmed, ya sanar da cewa dan takarar PDP, Zidon Nzanyopwa, ya yi nasara bayan samun kuri’u 19,174.
Nzanyopwa ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Bio Alexander, wanda ya samu kuri’u 5,676 kacal.
Bayan bayyana sakamakon Numan, Hukumar Zabe ADSIEC ta tabbatar da cewa PDP ta kammala mamaye dukkan kananan hukumomi 21 na jihar.
Shugaban ADSIEC, Mohammed Umar, yayin da yake sanar da sakamakon gaba daya a Yola, ya ce ‘yan takarar PDP sun lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi da kuma kujerun kansiloli 226.
Umar ya gode wa al’ummar Adamawa saboda fitowa domin amfani da hakkinsu na kada kuri’a, sannan ya bukaci ‘yan takara da jam’iyyun da suka sha kaye su amince da sakamakon zaben cikin kwanciyar hankali.
Wannan nasara na nufin PDP za ta ci gaba da rike madafun iko a matakin kananan hukumomi a jihar Adamawa, duk da cewa jihar yanzu tana karkashin jagorancin gwamnan APC.
Lamarin ya zo ne bayan sauya sheka da Gwamna Ahmadu Fintiri ya yi daga PDP zuwa APC. Sai dai an riga an tantance da kuma amincewa da ‘yan takarar PDP na zaben kananan hukumomin tun kafin sauya shekar gwamnan a farkon shekarar nan.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t