Fashi Barnar Aiki: Iran ta yiwa sansanin sojin saman Isra’ila luguden wuta a Nazareth

IMG 110400 08626 1780913054533

Isra’ila ta sanar da kai hare-hare a tsakiya da kuma yammacin Iran, duk kuwa da gargaɗin da shugaban Amurka Donald Trump yayiwa Prime ministan ƙasar Benjamin Natenyahu na ya dakatar da kai harin.

Wannan ba shi ne karon farko da Trump ke yiwa Natenyahu gargaɗin ƙauracewa kai hare-hare, tare a bada damar buɗe tattaunawar da zata kawo ƙarshen wannan yaƙi musamman a Lebanon ba.

Sa’o’i bayan kai harin, Trump ya ce wannan ba zai dakatar da yunƙurinsa na shiga tattaunawa mai ma’ana da Iran don kawo ƙarshen taƙaddamar ba.

Ko a makon da ya gabata an jiyo yadda Trump ya yi kacha-kacha da Natenyahu yayin tattaunawarsu ta wayar tarho kan yadda yake nuna taurin kai, a game da batun samar da ingantacciyar yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsa da ƙasashen Lebanon da kuma Iran.

Bayanai sun nuna cewa tuni Iran ta mayar da martani kan wannan hari, matakin da ba shakka zai dakatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da Trump ke fatan ƙullawa da Iran.

Dakarun Iran sun ce sun kai hari, sansanin rundunar sojin sama ta Isra’ila da ke Nazareth, duk da cewa dakarun Isra’ila sun yi iƙirarin dakatar da wasu makamai masu linzami da Iran da jefawa ƙasar.

RFI Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *