Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da sare bishiyoyi a harabar Abubakar Rimi Television (ARTV), bayan rahoton da The Historica Nigeria ta wallafa kan zarge-zargen sare bishiyoyi da kuma damuwar al’ummar Hotoro da kewaye.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayar da umarnin ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai tashar talabijin din.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ameen Kabeer Yassar, ya sanya wa hannu, Kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta da ke nuna yadda ake sare bishiyoyi a harabar tashar.
Ya ce daga yanzu babu wata bishiya da za a sake sarewa a ARTV ba tare da amincewar hukumomin da ke da alhakin kula da muhalli da gandun daji ba.
Baya ga batun muhalli, Kwamishinan ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ayyukan tashar suka ragu, inda ya ce ARTV na bukatar sabunta kayan aiki, horas da ma’aikata da kuma rungumar tsarin yada labarai na zamani domin ta iya gogayya da sauran tashoshin talabijin na zamani.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t