Nijeriya tana cikin tattaunawa da Amurka bayan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan zargin ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya ce.
A farkon Nuwamba 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ‘yan ta’adda suna tsananta wa Kiristoci a Najeriya, zargin da Abuja ta musanta.
“Abin da muke tattaunawa shi ne yadda za mu yi aiki tare don magance kalubalen tsaro wadanda suka shafi duniya baki daya,” in ji Minista Yusuf Tuggar a wata hira a babban birnin tarayya Abuja.
A farkon watan Nuwamba Trump ya ce ya bukaci Hedikwatar Tsaro ta Amurka, Pentagon ta tsara wata yiwuwar shirin kai hari a kasar wadda ta fi yawan jama’a a Afirka, saboda ‘yan ta’adda suna “kashe Kiristoci sosai.”
Da aka tambaye shi ko yana ganin Washington za ta tura sojoji su kai farmaki, Tuggar ya ce: “A’a, bana tunanin haka.”
Shugaban Amurka ya ce addinin Kiristanci na fuskantar “barazanar kawar da shi” a kasar ta Yammacin Afirka, inda ya yi gargaษi cewa idan Nijeriya ba ta dakatar da kashe-kashen ba, Amurka za ta kai hari kuma “zai kasance cikin sauri kuma mai tsanani.”
Nijeriya, wacce ke da mutane kimanin miliyan 230, an raba ta kusan daidai tsakanin kudu mai rinjaye Kiristoci da arewa inda Musulmai suke da rinjaye.
Ta’addanci a Nijeriya yana shafar Kiristoci da Musulmai duka, ba tare da bambanci ba.
TRT Afrika Hausa.
About advertisement or advice call this Number +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news Fallow here ๐
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t