Hukumomin Chadi sun kama Muslim Muhammad Yusuf, ɗan marigayi shugaban Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf, tare da wasu mutane biyar yayin da yake jagorantar wani rukunin ISWAP.
Bincike daga abokan iyali da danginsa ya tabbatar cewa Muslim ɗan Bintu ne, matar farko kuma babbar matar marigayi Muhammad Yusuf kamar yadda mai sharhi kan Lamuran tsaro, Audu Bulama Bakarti ya tabbatar a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X.
Acewar bayanin, an kiyasta cewa yanzu yaron yana da shekara 18 zuwa 19, abin da ya yi daidai da rahoton hukumomin Chadi.
An ce an kama shi ne bayan bayanan leken asiri daga Najeriya, a makon da Najeriya ta sanar da cafke manyan shugabannin ƙungiyar Ansaru da kuma shugaban ƙungiyar Mahmuda.
Masana tsaro sun bayyana cewa wannan na nuna sabon ci gaba wajen yaƙi da ta’addanci, duk da haka sun yi kira ga gwamnati ta maida hankali kan yaƙar ‘yan fashin daji a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, wadanda ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t