Da Dumi Duminsa: An kwashe namun dajin gidan tsohon Akanta na Ƙasa

IMG 115215 28725 1753699949271

Shugaban gidan adana namun daji na Kano, Sadik Kura Muhammad, ya tabbatar da cewa an kama babban maciji nau’in python da ya tsere daga gidan tsohon Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris, inda aka mayar da shi tare da wasu namun daji zuwa gidan adana namun dajin Kano.

Ɓacewar macijin ya tayar da hankula a unguwannin Daneji da kewaye a jihar Kano. Daga cikin sauran namun daji da aka gano a gidan Idris akwai kada da kuma ƙaramin damisa.

Maƙwabtan yankunan Daneji, Mandawari, Kabara da Soron Dinki sun bayyana cewa sun kasa samun natsuwa har sai da aka kama macijin aka fitar da shi daga yankin.

A wata hira da ya yi da gidan rediyo a Kano, Sadik Kura Muhammad, ya ce bayan fargaba da tashin hankali da lamarin ya jawo, tsohon Akanta Janar ɗin da kansa ya mika duka namun dajin dake gidan sa zuwa gidan Zoo, inda ake tsare da su yanzu.

Muhammad ya bayyana cewa Idris na da lasisin da ya halatta masa riƙe irin waɗannan namun daji a gidansa, kuma ba su kai wani mataki da za su zama barazana ba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin, kuma an gayyaci Ahmed Idris domin amsa tambayoyi.

Dailynews

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *