Daga Aminu Bala Madobi
Sufeto Janar na Ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce ba shi da hurumin cire jami’ansa daga ckin shirin fanshon da suke korafi a kai, duk da ya ke ya na buƙatar ganin an inganta rayuwar su saboda gudumawar da suka bayar.
Egbetokun wanda yake mayar da martani a kan zanga zangar da tsoffin jami’an hukumar suka gudanar a jiya, wadda ta samu goyan bayan jama’a sosai saboda halin kuncin rayuwar da suka samu kan su, ya ce duk da ya na tausaya musu, amma ɗaukar matakin fitar da su daga tsarin fanshon ya fi karfin sa.
Sufeto Janar ɗin ya ce dukkan su suna cike da damuwa a kan tsarin, la’akari da yadda yake shafar rayuwar jami’an da suka sadaukar da ran su wajen yiwa kasa aiki, musamman ganin su ma nan gaba za su yi ritaya.
Egbetokun ya ce ya gana da mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, wanda ya jagoranci tattaunawa a kan yadda za’a inganta rayuwar tsoffin jami’an.
Sufeto Janar din ya ce duk da ya ke ba zai bayyana irin matakan da aka cimma ba a bainar jama’a, zai bada tabbacin cewar an kama hanyar magance matsalar ta dindindin.
Egbetokun ya kuma janyo hankalin tsoffin jami’an da su kaucewa bari wasu na amfani da su domin cimma burin su.
Dangane da ficewa daga tsarin fanshon gaba ɗaya kuma, Sufeto Janar din ya ce duk da yake ba ya adawa da buƙatar, amma ta fi karfin ofishinsa, yayin da yake jaddada na goyan bayan tsoffin jami’an.
Egbetokun ya ce sun kwashe shekaru 11 su na gabatar da wannan buƙata, amma hakan bai yiwu ba.
RFI Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD