Na cika kashi 85% na alƙawuran da na ɗauka a lokacin yakin neman zabe na – Ina Ji Gwamna Kano

FB IMG 1752844205624

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawuran da ta dauka wa al’ummar jihar, inda ya rage kashi 15 cikin 100 yayin da yake shiga shekara ta biyu na wa’adin mulkinsa na farko.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke rantsar da sabon Shugaban Ma’aikata na Jihar, Dr Sulaiman Wali Sani; Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (mai ritaya), da kuma Masu Ba da Shawara na Musamman guda 11, a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa wannan nasara ta kasance sakamakon tantancewar da aka yi kan ayyukan gwamnatinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

“Na yi farin ciki cewa makon da ya gabata lokacin da na duba wuraren da muka samu kuri’a a zabe, duk alkawuran da muka yi wa jama’a, a cikin shekaru biyu mun aiwatar da kashi 85 cikin 100. Don haka, yanzu ya rage mana kashi 15% kawai da za mu aiwatar cikin shekaru biyu masu zuwa, insha Allah,” in ji shi.

“Mun gabatar da wannan batu a gaban Majalisar Zartaswa ta Jihar. Mun dubi yadda abubuwa ke gudana kuma muna da shekaru biyu a gaba. Don haka za mu duba hanyoyin da za mu tabbatar da cika wannan kashi 15%,” inji shi.

Gwamna Yusuf ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo sababbin tsare-tsare da shirye-shirye domin kara tasiri a rayuwar al’ummar jihar Kano.

“Muna kawo sababbin shirye-shirye da ayyuka wadanda, da yardar Allah (SWT), za su ci gaba da inganta rayuwar al’ummar jihar. Kuma ba za mu iya yin hakan mu kadai ba; dole ne mu hada kai da ku duka,” in ji shi.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *