Rundunar Yan sandan jihar Kano ta ce tana sane da taƙaddamar da ke tattare da irin salon wa’azin Lawal Triumph wanda ya janyo sa-in-sa a tsakanin al’ummar jihar ta Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, yace ƴan sandan sun ce duk da cewa malamin yana da ƴancin faɗin albarkacin bakinsa, to amma “muna da hurumin ganin mun tabbatar da anyi komai bisa doka da oda”
Hakan ne ya sa kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Kano ya gayyaci malamin tare da shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar kamar jami’an gwamnati da jagororin addini da na al’umma domin ganin yadda za a daƙile ci gaba da bazuwar irin wannan rikici a nan gaba.
Rundunar ta nemi dukkannin ɓangarorin al’umma da su kai zuciya nesa da gujewa faruwar abubuwan da ka iya rura wutar rikicin.
“Yana da matuƙar amfani a girmama fahimta da abin da jama’a suka yi imanin da shi sannan kuma a tabbatar duk abin da mutum zai yi ka da ya ƙetare iyakar shari’a.” In ji rundunar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD