Gwamna Abba Ya Hori Jami’an SSR Da SR Da Suyi Amfani Da Ilimin Da Suka Samu Wajen Gabatar Da Ayyukansu Cikin Aminci

FB IMG 1715254046724

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ta bakin sakataren gwamnatin jihar ya hori Jami’an SSR sa SR suyi amfani da Ilimin da suka samu, wajen gabatar da ayyukansu cikin aminci.

Hakazalika gwamnan ya yabawa ma’aikatar yaษ—a labarai da ayyukan cikin gida musamman Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya duba da yadda yake kokarin zakulo abubuwan da zasu kawowa Kano cigaba da al’ummar jihar.

Gwamnan ya ce, zan yi amfani da wannan dama domin na sanar daku cewa, gwamnatinmu ta Kano ta gasganta cewar samun sahinan bayanai da ilimi na taimakawa wajen cigaban al’umma, na horeku da kuyi amfani da wannan ilimi da kuka samu wajen aikinku na yau da kullum.

Ina kuma yabawa wadanda suka bada wannan horo domin samun ingantacciyar kwarewa, don haka na ayyana rufe wannan taro na kwana hudu a hukumance, Allah ya taimaki jihar Kano da al’ummata ameen.

A jiya Alhamis 10/7/2025 aka kammala bawa SSR da SR na jahar kano bita ta musanman damin basu horo yadda zasu samu kwarewa wajan gudanar da aikin su.

Taron an yi shine bisa ษ—aukar nauyin gwamnan jahar Kano karkashin jagorancin Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Camarde Ibrahim Abdullahi waiya.

Sama da mutun dari ne suka Amfana da wannan  horo tsakanin Mata da maza domin samun kwarewa a fannin aikin watsa labarai.

A nasa jawabin kwamishinan yaษ—a labarai da ayyukan cikin gida Camarde Ibrahim Abdullahi Waiya ya ja hankalin su, akan su rike aikin su da gaskiya da Amana, ya kuma kara da cewar, Alhamdulillah yau rana ce ta farin ciki da murna, domin duk abinda muke hasashe ya tabbata bayan Fara wannan horon kuma yau gashi an kammala shi.

Waiya ya kuma ce, idan ka kalli fuskokin mahalarta wannan bitar zaka tabbatar da cewar suna cikin aminci, yanzu haka ko baka ce musu yan jarida ba zaka iya kiransu kannen yan jaridun duba da yadda aka basu wannan horo daga gaggun malaman aikin jarida.

Kwamishinan ya yabawa gwamnan jihar kano bisa Yadda Yake kawowa al’ummar jahar cigaban ta fanni daban da daban.

A karshe yayi musu fatan Alkairi akan Allah ya dafa musu su yi ayyukansu cikin gaskiya da aminci.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan ๐Ÿ‘‡

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *