Daga Aminu Bala Madobi
Sashin Yanar Gizon Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya lalace sakamakon cikowa yayin da ‘yan Najeriya da dama suka mamaye dandalin domin shiga sabuwar jam’iyyar ta hadin gwiwa.
A wani sako a ranar Juma’ar da ta gabata, wani mai amfani da shi ya ce wannan ci gaban na zuwa ne yayin da bukatar mambobin da ke bukatar shiga cikin sabuwar Jam’iyyar ke ta rige-rige domin shiga Jam’iyyar ceto.
Jaridar IntelRegion ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace shafin ya samu tangarda a yayin da jama’a ke tururuwa domin shiga sabuwar Jam’iyyar hadakar.
Tangardar fasaha na nuna cewa rukunin yanar gizon ya gaza ƙarfin ikon rike cunkoson mutanen dake kokarin shiga shafin
Sai dai har yanzu jam’iyyar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan ci gaban ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Lamarin na zuwa kwanaki biyu bayan kaddamar da jam’iyyar ADC, a matsayin sabuwar jam’iyyar adawa ta hadaka wadda ke da aniyar kawar da jam’iyyar APC mai mulki da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Wani mai amfani da Facebook, Unclè Anass Dukura, ya ba da rahoton ganin saƙonnin tangarda ko rashin iya loda shafin.
“Bukatar mutane ta girme adadin yadda aka tsara dandalin”
A ranar Laraba ne aka kaddamar da jam’iyyar ADC a Abuja a matsayin dandalin kawancen Jam’iyyun ‘yan adawa a Najeriya.
Wasu daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar ADC sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark; Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Argegbesola, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi.
Sauran wadanda suka halarci bikin kaddamarwar sun hada da: Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, John Oyegun, Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, Tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, Dino Melaye, tsohon Ministan Matasa da Wasanni; Solomon Dalong; Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe na jam’iyyar Labour (LP), tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, tsohon babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya).
Tun da farko dai ana kiran jam’iyyar Alliance for Democratic Change a shekarar 2005, amma sai aka sauya mata suna zuwa African Democratic Congress a lokacin da aka yi wa jam’iyyar rijista da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC).
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD