Iran ta wallafa ragowar jirgin Hermes-900 na Isra’ila wanda ya kakkabo lokacin da yake shawagin leken asiri a birnin Tehran….
KARIN BAYANI AKAN JIRGIN HERMES-900
Jirgin Hermes-900, wanda kamfanin Elbit Systems na Isra’ila ta kera, na ɗaya daga cikin jirage marasa matuƙi mafi ƙarfi a duniya. An ƙera shi don leƙen asiri, sa ido, da kai hari, yana aiki a sararin samaniya har tsawon ƙafa 30,000 kuma yana iya aiki har na awanni 36 ba tare da ya tsaya ba..
Yana dauke da kyamarori masu ƙarfi da radar don tura bayanai kai tsaye, yana iya ɗaukar makamai masu nauyi kamar irin makamin “Spike”. yana da karfin sadarwa mai nisa har kilomita 1,500…
Bayan kasar Isra’ila da ta kera jirgin akwai wasu kasashe da suke amfani dashi irin su India da Argentina da sauransu, sai da na India ya fado a shekarar 2024 lokacin da yake zagayen leken asiri a Pakistan….
Masana na bayyana cewar harbo jirgin Hermes-900 da Iran tayi a wannan lokacin, ya nuna irin ilmin da take dashi a bangaren saka idanu a sararin samaniya .


Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD