Kungiyar Yan Jaridu Ta Kasa  (NUJ) Ta Karrama Gwamnan Kano A Bikin Cikarta Shekaru 70

FB IMG 1750580366543

Ƙungiyar Ƴan Jaridun kasa (NUJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta musamman bisa goyon bayan da yake bai wa aikin jaridu.

‎An bayar da lambar karramawar ne a wani biki da NUJ ta shirya domin cikarya shekaru 70 da kafuwarta a Abuja, inda mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karɓa a madadin gwamnan.

‎Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Muhammad Idris, ne ya miƙa lambar girmamawar.

‎Shugaban NUJ na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya ce an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin goyon bayan da yake bai wa kafafen yaɗa labarai da kuma jajircewarsa wajen cigaban ƙasa, kare ’yancin fadar albarkacin baki da inganta shugabanci na gari.

‎A nasa jawabin, mataimakin gwamnan ya taya Gwamna Abba murna, yana mai cewa karramawar ta nuna yadda gwamnatin Kano ke mutunta aikin jarida da ma dimokuraɗiyya baki ɗaya.

‎Kwamared Gwarzo ya kuma bayyana cewa Jihar Kano za ta karɓi bakuncin taron Kungiyar NUJ na gaba, idan Allah ya kaimu.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *