Sa’insa Akan Budurwa Ta Kaiga Hallaka Wani Saurayi A Jihar Neja.

IMG 20250611 WA0591

Daga Aminu Bala Madobi

Saurayin mai suna Usman Mohammed da ke zaune a unguwar Barikin-Sale a garin Minna a jihar Neja, ya gamu da ajalinsa bayan wasu gungun mutane uku masu suna Barafi, Ayya da kuma wani mutum daya da har yanzu ba a san sunan sa ba, bayan wata arangama da suka yi da budurwar sa.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin lokacin da Usman ya je domin hira da budurwarsa, Halima Usman, a Deeper Life Upper Base da ke yankin.

Ayayin da su biyun ke zaune a waje suna ta hira abin su, sai mutanen uku suka tunkare su ana zarginsu da yunkurin lallashin Halima domin ta canza raayin ta zuwa abokin su.

Jaridar Alfijir ta rawaito cewa mutanen sun ba ta Naira 5,000 don su fita da su, amma ta ki karba. Lamarin ya rikide zuwa tashin hankali, wanda ya kai ga daya daga cikin mutanen ya daba wa Usman wuka a baya.

Bayanai sunce an garzaya da shi babban asibitin garin Minna domin ba shi agajin gaggawa, amma rai yayi halin sa a safiyar ranar Talata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, ya kuma ce ana cigaba da gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *