Buratai ya sha da kyar a harin da ake zargi ƴan Boko Haram sun kai masa a Borno

FB IMG 1749474221680

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’a bayan da mayakan Boko Haram suka farmaki ayarin motarsa a Jihar Borno.

PUNCH ta ruwaito cewa Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin din Channels a daren Lahadi.

A cewar Ndume, tsohon Janar din da sojojin da ke tare da shi sun fada cikin kwanton bauna ne a kusa da wata barikin sojoji .

Ko da yake ba a tantance adadin asarar rayuka ba, Ndume ya bayyana cewa  musayar wuta ta barke tsakanin masu harin da sojojin da ke raka Buratai.

“Muna cikin mawuyacin hali na tsaro. Kwana biyu da suka wuce, an kai wa Buratai hari a sansanin sojoji a  Borno.

“Jami’ansa sun mayar da martani cikin jarumta, amma ‘yan ta’addan sun lalata wasu kayan aikin sojoji,” in ji shi.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *