Jami’an NDLEA sun Kama mutane 36 kan laifikan safarar kwayoyi daban-daban a Kano

FB IMG 1735210470636

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta cafke mutum 36 bisa zargin safarar nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban a wani gagarumin samame da ta gudanar a sassan jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa samamen ya gudana ne a ranakun 30 da 31 ga watan Mayu.

Ya ce daga cikin wuraren da jami’an suka kai samame akwai Maƙabartar Ɗan’agundi, kasuwar Kwari, Ƙofar Na’isa da kuma Kano Line — dukkansu kafin lokacin bukukuwan Sallah.

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne tare da buhunan tabar wiwi, sukurkudan sukudaye, diazepam, sholisho da sauran sinadarai da doka ta haramta.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Kwamanda Abubakar Idris-Ahmad, ya jinjinawa jami’an da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar samamen, tare da bukatar al’umma su yi bikin Sallah cikin kwanciyar hankali da natsuwa ba tare da amfani da ƙwayoyi ba.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bayar da rahoto kan duk wani motsi da ake zargin yana da nasaba da fataucin miyagun ƙwayoyi, domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma da zaman lafiya a jihar.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *