Hukumar tace finafinai ta dakatar da haska shirin Labarina, Gidan Sarauta da Dadin Kowa da wasu fina-finai 18

FB IMG 1747492521343

A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana’antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-Mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ka’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV

Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar take yawan karba dan kara inganta aiyukan Hukumar tare da masana’antar kannywood.

Abdullahi Sani Sulaiman shine jami’in yada labaran Hukumar ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:

Dakin Amarya
Mashahuri
Gidan Sarauta
Wasiyya
Tawakkaltu
Mijina
Wani Zamani
Labarina
Mallaka
Kudin Ruwa
Boka Ko Malam
Wa yasan Gobe
Rana Dubu
Manyan Mata
Fatake
Gwarwashi
Jamilun Jiddan
Shahadar Nabila
Dadin Kowa
Tabarma
Kishiyata
Rigar Aro

Ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar tace duk wani film tare da lura da ayyukan ‘yan masana’antar kannywood matsawar suna da rejista da Hukumar a ko ina suke.

A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen TV ko kafar internet.

Haka kuma ana sanar dasu cewa su miko fina-finansu ga Hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nan da sati daya mai zuwa wato daga Litinin, 18 ga watan Mayy, 2025 zuwa 25 ga Mayu, 2025 domin gujewa fushin doka.

A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gidajen TV da Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimakawa Hukumarsa domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *