Da Dumi Duminsa: Gwamna Kano ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar

1001308788

Daga Aisha Salisu Ishaq

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Asabar.

Nadin Ibrahim zai fara aiki daga ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025.

Sanarwar ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa gogewar da yake da ita, wanda ake sa ran zai yi amfani da ita wajen inganta harkokin gwamnatin jihar Kano.

Umar Farouk Ibrahim ya haura shekaru talatin yana aikin gwamnati , don haka ake fatan zai kawo cigaba sosai a shaโ€™anin tafiyar da harkokin aikin gwamnati.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan ๐Ÿ‘‡

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *