Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otal da ke ƙasar Koriya ta Kudu.
Alfijir labarai ta rawaito gobarar ta tashi ne a hawa na tara a benen otal ɗin da ke birnin Bucheon. Biyu daga cikin waɗanda suka mutu sun yi tsalle ne daga taga.
Haka nan kuma jami’ai a yankin sun ce an samu gawar wasu mutanen a matattakalar otal ɗin
Ana kula da lafiyar mutum 12 da suka samu rauni – waɗanda da dama na cikin mawuyacin hali.
Ana binciken musabbabin tashin gobarar.
Duk da cewa gobarar ba ta yaɗu ba, ta yi ɓarna sosai saboda ɗakunan otal ɗin ba su da abubuwan kashe gobara.
Ƴansanda suna gudanar da binciken musabbabin gobarar, da kuma ko akwai sakacin masu otal ɗin.
RN