Sama Da Biliyan 50 Da Aka Sace A Asusun Gwamnatin jihar Kano Aka Boye A Dubai Da London – In Ji Muhuyi

FB IMG 1723451524620

An gano kaddarorin da ke da alaƙa da wannan satar a Dubai, London, da Abuja, ciki har da otal-otal.”

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa hukumar ta gano sama da Naira biliyan 50 da aka sace daga asusun gwamnatin jihar da kananan hukumomin jihar.

Rimin Gado ya bayyana wani lamari na musamman inda ake zargin an karkatar da Naira miliyan 450 da sunan sayen gidajen sauro. Ya kara da cewa wanda ake zargin ya nemi a dakatar da hukumar daga Abuja bayan wani bincike da aka yi.

Da yake jawabi a wani taron karawa juna ilimi da aka yi wa manyan ma’aikatan gwamnati kan yaki da cin hanci da rashawa a karshen mako, Shugaban ya bayyana cewa, “Mun gano sama da Naira biliyan 50 da aka sace a baitul mali, tare da shaidu kusan 145. Mun gano kaddarorin da ke da alaka da wannan satar a Dubai, London, da Abuja, ciki har da otal-otal.”

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC a Kano, Ibrahim Garba Kagara, ya yabawa hukumar PCACC kan farfado da yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

CSP Aminu Bashir, wanda ke wakiltar Daraktan shiyya na EFCC, ya goyi bayan wannan ra’ayi, inda ya bayyana cewa kashi 95% na almundahana ya samo asali ne daga saye. Ya shawarci ma’aikatan gwamnati da su bi dokokin sayan kaya don gujewa matsalolin da suka shafi doka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya jaddada cewa ba za a iya yin zamba ba tare da hadin gwiwar ma’aikatan gwamnati ba. Ya yi gargadin cewa gwamnati mai ci ba ta da hurumin cin hanci da rashawa, ya kuma koka da yadda jihar Kano ta fuskanci cin hanci da rashawa a cikin shekaru takwas da suka gabata, wanda ya kawo cikas ga ci gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *