Ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatocin tarayya ta janye takardarta mai dauke da kwanan watan Agusta 1, 2024, wadda ta bayyana yadda ake sayar da buhunan shinkafa mai nauyin kilo 50 ga ma’aikatan Gwamnati akan Naira 40,000.
Alfijir labarai ta ruwaito Aderonke A. Jaiyesimi, Daraktan Kula da Ma’aikata ne ya sanar da janyewar a cikin wani sabon umarni. Ta ce, “An umurce ni da in koma ga takardar mu ta cikin gida ta ranar 1 ga Agusta, 2024, kan batun da ke sama kuma in sanar da ku cewa an janye da’awar.”
A baya gwamnatin Najeriya ta umurci ma’aikatanta da su cike fom don siyan buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan Naira 40,000, a wani mataki na rage matsalar abinci da ke addabar al’ummar kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj