Ibtila’i! Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama Da 200 A Jihar Kebbi

IMG 20240805 WA0057

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankuna uku a karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi, inda ta lalata gidaje sama da 200.

Alfijir labarai ta ruwaito Ambaliyar ta afku ne a ranakun Asabar da Lahadi, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi, wanda ya shafi kauyukan Bayawa, Tiggi, Fakon Sarki Settlement, da Unguwar KARDA a cikin garin.

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar, wanda ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa, domin tantance irin barnar da aka yi da kuma tallafa wa wadanda abin ya shafa, ya bayar da umarnin tantance gidajen da lamarin ya shafa kuma dukiyoyin da suka rasa cikin gaggawa.

Ya kuma ba da umarnin a kwashe mutanen zuwa makarantun da ke kusa da su domin kare lafiyarsu tare da ba da agajin gaggawa.

Ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan biyar ga kowane kauyen da abin ya shafa – Bayawa, Tiggi, da Fakon Sarki a matsayin tallafin farko da kuma Naira miliyan daya don siyan abinci da ruwan sha ga β€˜yan gudun hijirar.

Abubakar, ya tabbatar wa wadanda abin ya shafa da mika rahoton lamarin ga gwamnan jihar domin samun karin taimako daga gwamnatin jihar da ta tarayya.

Ambaliyar ta sa mutane da dama sun rasa matsuguni, inda wasu ke neman mafaka ta wucin gadi a makarantun da ke kusa.

RN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *