A yayin da ake shirin fara zanga-zanga a gobe Alhamis kan matsin tattalin arziki, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio yayi shagube ga masu shirya zanga zangar inda ya ce suna kan titi su kuma suna gida suna cin abinci.
Alfijir labarai ta ruwaito Akpabio ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da yake jawabi ga wakilan hukumar raya yankin Niger Delta a jihar Rivers.
Shugaban majalisar ya ce mutanen yankin Niger-Delta basu shirya sauya gwamnati ba.
“Dukkanin mu muna jin abinda ke faruwa a jikinmu. Amma mun sani zai zama na karamin lokaci ne. Mai girma MD ina so na gode ma kan abinda ka fada. Ka ce bamu fa bukatar sauya gwamnati. Kuzo mu rungumi wannan gwamnati.
” Wadanda ke son yin zanga-zanga, suje su yi. Amma mu muna nan zamu ci abincinmu. Dole ne na godewa al’ummar Niger-Delta.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj