Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Sabon Mafi Karancin Albashi

FB IMG 1719960146800

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu saba’in.

Alfijir labarai ta ruwaito da yake zantawa da manema labarai bayan rattaba hannun na shugaban kasa,  shugaban majalisar dattijai  Godswill Akpabio, ya bayyana jin dadinsa game da wannan ci gaba da aka samu, inda ya jaddada cewa sabon mafi karancin albashin ya shafi dukkan bangarori da suka hada da gwamnatin tarayya, jihohi, da kananan hukumomi, da kamfanoni masu zaman kansu.

Akpabio ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa na inganta rayuwar ma’aikatan Najeriya, inda ya bayyana cewa majalisar kasa ta gaggauta zartar da kudirin dokar ya zama doka saboda da goyon bayan su ga shirin.

Ya kuma yi fatan za .a gudanar da zanga-zanga cikin lumana, yana mai gargadi kan duk wani nau’i na tashin hankali tare da yin kira ga matasa da kada a yaudare su da manufofin siyasa da ke da nufin haifar da tarzoma.

Akpabio ya bada tabbacin cewa kudirin samar da kudade na tallafawa wannan karin albashi yana tafiya yadda ya kamata kuma ana sa ran za a sanya hannu a ranar Laraba.

Wannan mataki a cewar Akpabio, ya yi daidai da kokarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a kasa da kuma tallafa wa ‘yan kasar saboda kalubalen rayuwa da ake fuskanta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *