Allah ya yiwa SA’IN Katsina Alhaji Ahmadu na Funtua rasuwa yau talata 25/6/2024 bayan gajeriyar jinya
Marigayi Alhaji Ahmadu na Funtua Sa’in Katsina yayana ga Alhaji Sani Zangon Daura Dan Masanin Daura, Marigayi Alhaji Ahmadu na Funtua Sa’in Katsina yayi Shekaru hamsin da watannani yana rike da wannan babbar sarauta wanda shine ragowar hakimi da marigayi Sarkin katsina Usman Nagogo Dan Sarkin Katsina Muhammad Dikko Dan Durbi ya nada,
Marigayi Sa’in Katsina yana daya daga cikin ragowar manyan Arewa, babu shakka anyi babban rashi.
An yi jana’izar Sa’in Katsina Alh Amadu Na Funtua da Allah Ya yi wa rasuwa a jiya Alhamis
An gudanar da yi masa sallah a makarantar firamare ta Sararin Kuka dake kusa da gidansa cikin birnin Katsina
Daga cikin wadanda duka sallaci zana’idar tasa har da Sarkin Katsina Alh Dr Abdulmumini Kabir Usman
Allah Ya ji kansa Ya gafarta masa ameen ameen .


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj