Gwamna Ya Mika Taaziyyar Rasuwar Babban Malami Sheilkh Mode Abubakar

FB IMG 1719185685746

Gwaman jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana kaduwa akan rasuwar daya daga cikin mashahurran malaman addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Mode Abubakar.

Alfijir labarai ta ruwaito Gwaman ya bayyana rasuwar da cewa wani irin babban rashi ne ba wai ga iyalan marigayin ba, a’a har ma ga jiha da kasa baki daya.

Yace marigayin ya gudanar da ruyuwar sa ne a wajen karantar da mutane akida da kuma aikin Daawah don yada addinin Islama.

Gwamna Aliyu ya ce za’a ci gaba da tuna Ayukkan alkhairi da gwagwarmayar marigayin yayi na yada addinin musulunci a lungu da sako na jihar nan.

Alhaji Ahmed Aliyu ya roki Allah da ya karbi kyawawan ayukkan marigayin ya kuma shafe kura kuran sa.

Haka ma ya bukaci iyalan marigayin dasu dauki wannan rashi a matsayin wani abu daga Allah, yana mai rokon Allah da ya basu hakuri.

Kafin rasuwar sa dai Sheikh Mode Abubakar shine Babban limamin Masallacin Jumu’a na Makarantar Koyarda ilimin Alqurani da sauran ilmomuka ta sarkin musulmi Muhammadu Maccido.
Allah ya jikan shi da rahama yasa ya huta.

Abubakar Bawa
Sakataren hulda da Yan Jarida a fadar gwamnatin jihar sokoto ne ra sanya hannu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *