Daga Aminu Bala Madobi
Babban jagora mai kula da dakin Allah Ka’abah ya rasu, Dr. Saleh bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi
Ya rasu yana da Shekaru 109 a duniya, ya kuma shafe shekaru 77 yana hidimtawa Ka’abah.
Marigayin ya fito daga kabilar Shayb daga gidan Qusay bin Kilab, Zuri’ar su ce ke rike da makullin Ka’abah tun zamanin Jahiliyya har zuwan Manzon Allah S. A. W.
An sami takardama bayan fatahu Makka wanda har Allah ya saukar da Ayar Al Qur’ani dake goyon bayan kabilarsu akan mayar da makullin zuwa ga ɗan kabilarsu..
Wanda hakan yayi silar shigar da yawa daga cikin yan kabilarsu cikin addinin Musulunci.
Allah ya gafarta masa ya kyautata na mu zuwan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj