Wasu mahara da har lokacin hada wannan labarin ba a Tabbatar da adadinsu ba, sun bindige Malam Sai’idu Jikan Basa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na Mazabar Mai Dabino ta karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Alfijir Labarai ta rawaito DCL Hausa ta tabbatar mata da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:37 na Yammacin Laraba a kan hanyarsa daga Danmusa zuwa Mai Dabino.
Bayanai sun ce an kira jiga-jigan jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Danmusa zuwa wani taro a Hedikwatar karamar hukumar, inda daga kauyen Mai Dabino ya tafi Danmusa don halartar wannan taro.
Yana kan hanyarsa ta komawa Mai Dabino bayan Kammala taron, wannan ibtila’in ya faru da shi, da wani Mutumin kauyen Kokarawa da ya rago wa hanya zuwa kasuwar Mai Dabino da ke a ranar Larabar nan.
Majiyar ta ce an yi musu jana’iza bayan sallar la’asar Ɗin nan da yammacin Laraba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇