Gwamnan CBN Cardoso, Tare da Mataimakin Gwamna CBN kan manufofin tattalin arziki, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Sun jagoranci wani taro da masu zuba hannun jari na cibiyoyi a fadin kasuwanni masu tasowa A ƙasar Amurka,
Alfijir Labarai ta Rana ta 5 ta taron IMF/Bankin Duniya na bazara ta shaida babban bankin Najeriya CBN ya cigaba da Gudanar da dabarunsa da masu ruwa da tsaki, tare da mai da hankali kan karfafa kawancen tattalin arzikin Najeriya da tsara yanayin tattalin arzikin duniya. #Taron IMFSpring
A yayin zaman, mahalarta, ciki har da zaɓaɓɓun shugabannin kasuwanci, manyan jami’an Gwamnati, da abokan hulɗa, sun yi magana game da muhimman abubuwan da suka shafi tattalin arziki Sun kuma yi nazari kan dabarun inganta hadin Gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya.
Gwamna Cardoso, Tare da DG kan manufofin tattalin arziki, Mista Muhammad Sani Abdullahi, sun jagoranci taronne da masu zuba hannun jari na cibiyoyi a fadin kasuwanni masu tasowa, wanda kungiyar Jefferies ta shirya. Taron dai ya ba da damar yin musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin Najeriya, Tare da mayar da hankali kan manufofin kuɗi da musayar kuɗaɗen ƙasashen waje.


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk